• Labaran yau

  Ka fita wajen APC ka zakulo Ministocin ka – An fadawa Buhari


  Legit Hausa

  Wasu Bayin Allah a Najeriya sun fito sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zakulo wasu daga cikin Ministocinsa wannan karo daga wajen jam’iyyar sa ta APC mai mulkin kasar. Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Punch, wasu ‘yan gwagwarmaya da masana a kasar nan ne su kayi wannan kira ga shugaban kasa Buhari, a daidai lokacin da ake shirin kafa sabuwar gwamnati mai-ci a kusan fadin Najeriya.

  Moshood Erubami, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘Nigeria Voters Assembly’, ya nemi shugaba Buhari ya zabo wasu daga cikin wadanda yayi takarar kujerar shugaban kasa da su a zaben 2019, ya ba su ofishin Minista a gwamnatinsa.

  Erubami yake cewa akwai ‘Yan takarar da bai kamata Buhari yayi watsi da su ba domin zai ga aiki da cikawa idan ya ba su mukami. Daga cikin wadanda ake rokon a ba mukami akwai Oby Ezekwesili, Kingsley Moghalu da Yele Sowore.

  Wani Malamin harkar siyasa a wata jami’a a Jihar Ogun, Femi Otunbajo, ya bayyana cewa duk da abu ne mai kyau shugaba Buhari ya zakulo Ministocinsa daga wajen APC, sai dai zai yi wahala ‘Yan PDP su karbi tayin Minista daga Buhari.

  Farfesa Femi Otunbajo, yake cewa ganin yadda Abokin hamayya, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya shigar da kara a kotu yana ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben bana, zai yi wa manyan ‘Yan adawa su yarda su yi aiki a gwamnatin APC.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ka fita wajen APC ka zakulo Ministocin ka – An fadawa Buhari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });