• Labaran yau


  Jihar Zamfara: Yan bindiga sun hallaka mutane 17 kuma suka hana jana'izarsu


  Legit Hausa

  Wasu yan bindiga sun hallaka akalla mutane 17 a mumunan harin da suka kai kauyukan Zamfara uku dake karamar hukumar Birnin Magaji dake jihar Zamfara, Daily Trust ta samu rahoto. 

  Mazaunan sun bayyana cewa yan bindiga sun shigo garin kan babura ne ranar Asabar inda suka kai hari kauyan Gidan Kaso kuma suka kashe akalla mutane 7, sannan kuma suka hana gudanar da jana'izar matattun. Wani mazaunin garin, Tukur Yusuf, ya laburta cewa: 

  "Sun hana jama'a gudanar da Sallar Jana'izar matattun har sai lokacin da jami'an tsaro da yan banga suka kawo agaji kauyen." 

  Gabanin yanzu mazauna Gidan Kaso sun gudu daga muhallansu sakamakon hare-haren yan bindiga amma suka dawo kwanan nan. Hakazalika, yan bindigan sun kai farmaki kauyen Dambo ranar Lahadi inda suka hallaka mutane 4 kuma suka kwashe musu awaki. 

  Wani mai idon shaida yace: "Mutane bakwai daga kauyen Kokeya da suka kawo agaji kauyen Dambo sun gamu da ajalinsu a hannun yan bindigan. 

  An kashesu yayinda suka kokarin taimakawa wadanda harin ya shafa a garin Dan Dambo. An nemi jawabi daga bakin kakakin hukumar yan sandan jihar amma ba'a samu isa gareshi ba yayin wannan rahoto.
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Jihar Zamfara: Yan bindiga sun hallaka mutane 17 kuma suka hana jana'izarsu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama