Jihar Kano: Za'a damke mukarraban sarkin Kano 3


Legit Hausa

Hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano tana shirin garkame shugaban ma'aikatan sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, Alhaji Munir Sanusi, kan rashin gurfana gaban hukumar domin amsa tambayoyi. 

Kana za'a damke wasu ma'aikatan masarautar Kano biyu, Mujitaba Abba Sani da Sani Muhammad Kwaru, wadandan sukayi kunnen kashi kan gayyatar da hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yiwa sarkin Kano na badakalar N4bn. Hukumar ta shirya tsaf domin shigar da kara kotun Majistare a yau domin samun ikon damkesu, wani majiya a hukumar ya laburta. 

A labari mai kama da haka, Gammayar kungiyar yan Arewa masu rajin samar da cigaba da dimukradiyya, NADP ta soki lamirin mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, inda ta nemi yayi gaggawar yin murabus daga sarautar Kano don kare mutuncin masarautar. 

Kungiyar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu a karshen taronta daga gudanar a babban birnin tarayya Abuja, taron daya samu halartar wakilanta daga jahohi 18 a Arewacin Najeriya inda suka tattauna batun matsalar tsaro a Arewa da kuma rikicin masarautar Kano.

Haka zalika kungiyar ta jinjina ma namijin kokarin da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi na nada sabbin sarakunan gargajiya guda hudu masu daraja ta daya a jahar Kano, na Rano, Bichi, Karaye da Gaya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN