Jerin kananan hukumomin dake karkashin masarautun Kano 5 bayan Ganduje ya sa hannu


Legit Hausa

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar kafa sabbin masarautu guda hudu (4) da suka hada da Rano, Karaye, Gaya da Bichi. Bayan saka hannu a kan wannan sabuwar doka, gwamnatin Jihar Kano zata nada sabbin sarakuna na wannan masarautun hudu da kuma zana iya fadin kasar su, sannan kuma shi Sarkin Kano na yanzu Mallam Muhammadu Sanusi II zai zama Sabon Sarkin Birnin Kano da Kewaye.

Sarkin Birni da Kewaye na da kananen hukumomi guda 10 a karkashin sa da suka hada da 1- Kano Municipal 2- Fagge 3- Nasarawa 4- Gwale 5- Tarauni 6- Dala 7- Minjinir 8- Ungogo 9- Kumbotso 10- Dawakin Kudu Sarkin Rano kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka; 1- Rano 2- Bunkure 3- Takai 4- Kibiya 5- Sumaila 6- Doguwa 7- Kiru 8- Bebeji 9- Kura 10- Tudun Wada

Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka; 1.Gaya 2.Ajingi 3.Albasu 4.Wudil 5.Garko 6.Warawa 7.Gezawa 8.Gabasawa Sarkin Bichi kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka; 1- Bichi 2- Bagwai 3- Shanono 4- Tsanyawa 5- Kunci 6- Makoda 7- Danbatta 8- Dawakin Tofa 9- Tofa

Sarkin Karaye kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka; 1- Karaye 2- Rogo 3- Gwarzo 4- Madobi 5- Kano 6- Rimin Gado 7- Garun Mallam

Sarkin Birnin Kano da Kewaye Mallam Muhammadu Sanusi II shine zai zamu Shugaban majalisar zartarwa na Masarautun guda biyar, sannan kuma Sarkin Rano shi zai zama mataimakin sa.

Sannan shugabancin wannan majalisar zai zamu na karba karba ne wato rotational inda kowanne shugaba zai shekara biyu inda bayan kammalawar waainda sa kuma gwamnatin jiha na da hurumin kara masa wani waadin karo na biyu.

Sannan sauran yan majalisar masarautar sun hada da 1- Sakataren Gwamnatin Jiha 2- Kwamishinan Kananen Hukumomi 3- Ciyamomin Mulki na kananen hukumomin 4- Hakimai masu nada Sarki bibiyu saga kowacce Masarauta. 5- Wakilcin mutum 5 da Gwamna zai nada. Daga karshe kuma sabuwar dokar bata hana wani wanda ya gaji Sarautar Kano daga sauran sababbin masarautun guda hudu ba, zama Sarkin Birnin Kano da Kewaye indai har sun gada.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN