Legit Hausa
Tsohon mataimakin shugaban kasar
Najeriya, Atiku Abubakar, yayi magana a yau 5 ga Watan Mayu 2010 domin tunawa
da Marigayi shugaban kasa Ummaru ‘Yaradua da ya rasu a irin wannan rana.
Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana
cewa mai matukar alfahari da cewa jam’iyyarsa ta PDP ce ta fito da Marigayi
Ummaru Musa ‘Yaradua. Shugaba ‘Yaradua ya rasu ne Ranar 5 ga Watan Mayun 2010
lokacin yana kan mulki.
Atiku Abubakar yake bayyana shugaba
Ummaru ‘Yaradua da shugaba kuma mutumin kirki. Atiku yace Marigayin ya kasance
mai hangen nesa wanda ya kawo zaman lafiya a yankin Neja-Delta mai arzikin man
fetur a Najeriya.
‘Yaradua yayi kokarin ganin wanzuwar
zaman lafiya a Neja-Delta inda ake fama da rikici bayan ya kawo wani tsari na
yi wa Tsageru afuwa. Atiku ya kara da cewa ya shaku da tsohon shugaban kasar a
siyasa a lokacin yana raye.
Atiku yake cewa da shi da Ummaru
‘Yaradua duk sun koyi karatun siyasa ne a wajen Maigidan sa Marigayi Janar
Shehu Musa Yar’Adua. Atiku yace tsohon Sojan ne ya koya masu yadda ake wanke
allon siyasa tun a shekarun baya.
Bayan haka kuma, ‘dan takarar
shugaban kasar na PDP a zaben bana yace yayi aiki da Ummaru ‘Yaradua sosai a
lokacin yana mataimakin shugaban kasa, a wancan lokaci shi kuma Marigayi Ummaru
‘Yar’adua yana gwamnan Katsina.
‘Dan siyasar ya bayyana irin
nasarorin da ‘Yaradua ya samu a lokacin yana mulki, musamman a bangaren
tattalin arziki da harkar mai. A karshe, Atiku yace ‘Yaradua ya san tsarin
mulki, yana mai masa addu’ar samun gidan Aljanna.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI