Legit Hausa
A yanzu haka, Mukaddashin Sufeto
Janar na yan sanda, Moammed Adamu na cikin zauren majalisar dattawa, inda yake
koro wa yan majalisar tarayya jawabai akan halin da tsaron kasar ke ciki.
Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa Adamu ya fara ziyartan ofisin babban mai ba
shugaban kasa shawara a harkokin majalisar dokoki (majalisar dattawa), Ita
Enang.
Legit.ng ta tattaro cewa yan
majalisar sun gayyaci IGP da farko sakamakon halin da tsaron kasar ke ciki.
Wannan shine karo na farko da shugaban yan sanda mai ci ya gurfana a gaban
majalisar dattawa tun 2014.
Ku tuna cewa Legit.ng ta ruwaito
cewa Inspekto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Alhamis, 25 ga watan
Afrilu ya janye tsarin rabe-raben aiki na rundunar yan sandan Najeriya.
A halin da ake ciki, Legit.ng ta
rahoto a baya cewa, Wasu kungiyoyi biyu dake rajin tabbatar da mulki nagari a
Najeriya, CD da CACOL sun ce matukar gwamnatin tarayya ta bar harkokin tsaro a
yankin arewa maso yamma suka cigaba da tabarbarewa, babu shakka nan ba da
dadewa ba 'yan bindiga zasu kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari hari ko kuma
ma su sace shi.
Kungiyoyin biyu sun bayyana hakan ne
a wata hira daban-daban da jaridar Punch tayi da su. Shugaban kungiyar CD na
kasa, Usman Abdul, ya ce, "bari na fada muku, da a ce shugaba Buhari ya na
garin Daura ranar da 'yan bindiga suka kai hari, zasu iya sace shi."
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI