Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta yi gargadi ga kwamishinan yansanda CP Wakili


Legit Hausa

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA ta gargadi kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Muhammadu Wakili kan ya fita daga sha’anin yaki da fataucin miyagun kwayoyi ko kuma ya fuskanci hukuncin shari’a.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Ibrahim Abdul yace, “ sashe na 3 (1) na kundin dokokin hukumar NDLEA ya basu damar kasancewa jagoran dukkanin al’amura da suka shafi tu’ammali da muggan kwayoyi a Najeriya.” 

Wannan rashin jituwar dai ya zo ne sakamakon furucin da kwamishinan yayi na cewa jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar damke kwalayen tramadol 303 cikin makon da ya gabata a jihar Kano. 

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata, Abdul yace ‘yan sanda sun karbe wani magani mai suna “diclofenac” wanda ke maganin ciwo jiki amma ba tramadol ba. Kazalika, Abdul ya kara fayyace mana cewa irin hakan ya taba faruwa a watan Fabrairu inda hukumar yan sanda tayi ikirarin cewa ta karbe kwayar tramadol, ko da muka bincika sai muka samu ashe maganin zazzabin cizon sauro ne da wani makamancinsa. 

“ Irin hakan ya taba faruwa a watan Fabrairu inda yace sun kama mota biyu na tramadol. Ko da muka same shi sai yace mana ya tura da su zuwa NAFDAC. Da isar mu NAFDAC sai muka tarar da abu daban da wanda ya fada mana. 

“ Babu saniyar ware a shari’a ko ni idan na karya doka dole shari’a zatayi hukuncin mafi dacewa a kaina. Saboda haka ina kira ga hukumar yan sanda da sauran hukumomi da kowa ya tsaya matsayinsa banda wuce gona da iri yayin gudunar da ayyukansu.” Inji kwamandan.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN