Hukumar DSS ta saki shahararren Malamin Musulunci na Bauchi da ta tsare

Legit Hausa

Rundunar tsaro na sirri (DSS) ta saki shahararren malamin nan, Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi wanda ta tsare bayan ya amsa wasu yan tambayoyi da tayi masa. Malam Abdulaziz wanda ya kasance babban limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, ya shiga hannun DSS ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

Daya daga cikin mambobin majalisar daliban malamain, Muhammad Abdulkadir ya tabbatar das akin Malamin nasu a yau Juma’a, 17 ga watan Mayu. Ya kara da cewa, wannan kamun da aka yi wa Malaminsu zai kara masa daukake ne ma a idon duniya ba kuma tauye masa kimarsa ba. 

Muhammad Abdulkadir ya bayyana cewar zuwa yanzu dai ba su da wata masaniya kan ko hukumar tsaron ta gindaya wa Malaminsu wasu sharuda, ya dai tabbatar da cewar an sako shi kuma ya dawo cikin iyalansa lafiya ba tare da wani matsala ba. 

A baya mun ji cewa, hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta yi ram da wasu manyan Malaman addinin Musulunci a jahohin Katsina da Bauchi, Sheikh Aminu Usman inkiya Abu Ammar da kuma Ustaz Idris Abdulaziz biyo bayan gayyatar da hukumar tayi musu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kimanin kwanaki biyar da suka gabata ne hukumar DSS ta gayyaci Ustza Idris zuwa ofishinta dake jahar Bauchi domin amsa wasu tambayoyi, sai dai daga nan kuma suka yi awon gaba dashi zuwa babban birnin tarayya Abuja don cigaba da yi masa tambayoyi. 


DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN