Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin kishin ruwa a watan Ramadan

Legit Hausa A lokacin azumin watan Ramadan, yana da matukar muhimmanci mutum ya ci abinci mai gina jiki sannan ya sha ruwa ko abab...


Legit Hausa

A lokacin azumin watan Ramadan, yana da matukar muhimmanci mutum ya ci abinci mai gina jiki sannan ya sha ruwa ko ababen sha domin gusar da kishi yayin sahur da bayan bude baki. Kishin ruwa yana iya janyo mutuwar jiki, bushewar labba, kishi da ciwon kai. 

Hakan yasa ya ke da muhimmanci mutum ya rika shan ruwa da abubuwa masu dauke da ruwa a lokacin azumi. 

Duk da cewa mai azumi ba zai sha ruwa ba har sai faduwar rana, akwai wasu matakai da zai dauka domin rage kishin ruwa mai tsanani. 

1 - Guji shan ababen sha masu dauke da caffeine: Caffeine wani sinadari ne da ke cikin ganyen shayi, coffee da sauransu kuma yana sanya yawan fitsari wanda hakan ke fitar da ruwa da gishiri daga jikin dan Adam. Shan caffeine mai yawa zai sanya kishi sosai saboda haka zai fi dacewa mutum ya sha ruwa ko kuma kayan itatuwa yayin sahur da bude baki. 

2 - Ka bude baki da kayan marmari da ganyaye: Baya ga iganta lafiya da kayan itatuwa da ganyaye keyi, suna kuma taimakawa wurin magance kishi saboda jikin dan adam ya kan sarrafa su a hankali ne wanda hakan zai sa ba za aji kishi da wuri ba bayan cin kayan marmari da ganyaye.

3 - Guji yawan gishiri da yaji: Gishiri da yaji da kayan kamshi na girki suna kara sanya kishi saboda haka idan mutum zai yi girki sai da takaita gishiri, yaji da kayan kamshi. 

4 - A rika yin wanka da ruwan sanyi: Yin wanka da ruwan sanyi a lokacin watan Ramadan yana taimakawa mutum wurin rage jin kishin ruwa. Yin wankan yana rage zafin jikin mutum wanda hakan na nufin ba zai yi gumi sosai ba ya zubar da ruwan jikinsa. 

5 - Guji kwalkwalan ruwa mai yawa cikin kankanin lokaci: Shan ruwa mai yawa lokaci guda ya kan sanya mutum ya yi saurin fitsarar da ruwan saboda haka ya fi dacewa mutum ya rika shan ruwan kadan-kadan bayan an bude baki. 

6 - Takaita shiga rana ko wuri mai zafi sosai: Yana da wahala mai azumi ya kauracewa shiga rana ko wuri mai zafi baki daya amma yana kyau ayi kokarin kauracewa tsananin zafi. Zafi ya kan sanya gumi wanda hakan ke janyo kishin ruwa. Mutum ya rage yawo cikin rana ya rika zama a inuwa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
IDAN KA GAN WANI ABU NA FARUWA, HANZARTAB KA SANAR DA MU A ISYAKULABARI@GMAIL.COM
Name

'YANSANDA,1,AL-AJABI,22,AREWA,45,BIDIYO,147,BINCIKE,1,BIRNIN-KEBBI,375,BOLLYWOOD,2,BUHARI,10,DUNIYA,109,ENGLISH,27,FADAKARWA,126,FASAHA,14,FITACCEN LABARI,19,HOTO,175,HOTUNA,90,JAKAR MAGORI,1,LABARI,2979,NISHADI,282,OSCAR,2,Samaila Yombe,42,SANARWA,31,SHARHI,16,SIYASA,387,TARIHI,11,TSARO,353,WASANNI,18,
ltr
item
ISYAKU.COM: Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin kishin ruwa a watan Ramadan
Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin kishin ruwa a watan Ramadan
https://2.bp.blogspot.com/-FYZwmNtBQ7Y/XN7yHq6vzqI/AAAAAAAAV3c/OH8IIcwTIbgA6JtcXrDlsezMDVKeObk5wCLcBGAs/s1600/fruits.jpg
https://2.bp.blogspot.com/-FYZwmNtBQ7Y/XN7yHq6vzqI/AAAAAAAAV3c/OH8IIcwTIbgA6JtcXrDlsezMDVKeObk5wCLcBGAs/s72-c/fruits.jpg
ISYAKU.COM
https://www.isyaku.com/2019/05/hanyoyi-6-da-mutum-zai-kare-kansa-daga.html
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/
https://www.isyaku.com/2019/05/hanyoyi-6-da-mutum-zai-kare-kansa-daga.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy