Gwamnoni 12 da suka sauka daga kan kujerar mulki


Legit Hausa

Gwamnoni 12 ne suka sauka daga kan mulkin jihohinsu a jiya bayan wasu daga cikinsu sun kammala wa’adin mulki na shekara 8 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tsara. 

Da dama daga cikinsu wadanda suka cika wa’adin mulkin nasu na shekara 8 da ma wadanda suka sha kasa bayan sunyi wa’adi guda daya kacal sun mika karagar mulki zuwa ga sabbin gwamnoni domin cigaba daga inda suka tsaya. 

Gwamnonin da suka yi murabus sun hada da; Rochas Okorocha na Imo, Akinwunmi Ambode na Legas, Ibikunle Amosun na Ogun, Kashim Shettima na Borno da Jibrilla Bindow na Adamawa.
Bugu da kari akwai, Abubakar Bello na Neja, Muhammad Abdullahi Abubakar na Bauchi, Umaru Tanko Al-Makura na Nasarawa, Ibrahim Danwambo na Gombe, Abdulaziz Yari na Zamfara da kuma Ibrahim Gaidam na Yobe. 

Sabbin gwamnoni wadannan jihohin su ne: Ahmadu Fintiri (PDP, Adamawa), Bala Muhammad (PDP, Bauchi), Babagana Zulum (APC, Borno), Inuwa Yahaya (APC, Gombe), Emeka Ihedioha (PDP, Imo), Abdulrahman Abdulrazaq (APC, Kwara), Babajide Sanwo-Olu (APC, Legas), Abdullahi Sule (APC, Nasarawa), Dapo Abiodun (APC, Ogun), Seyi Makinde (PDP, Oyo), Mai-Mala Buni (APC, Yobe) da kuma Bello Matawalle (PDP, Zamfara).
 

 DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN