• Labaran yau


  Gwamnatin tarayya, jahohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan 617


  Legit Hausa

  Rabe raben gwamnatocin Najeriya guda uku da suka hada da gwamnatin tarayya, gwamnatin jahohi 36 da kuma gwamnatin kananan hukumomin 774 sun rabashe yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasafta musu jimillar kudi naira biiyan dari shida da goma sha bakai da miliyan hamsin da bakwai (N617,057,000,000).

  Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar kididdiga ta kasa ce ta sanar da wannan alkalumma cikin wani rahoto data fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, inda tace an samu wadannan kudade ne a watan Maris, kuma aka rabma ma gwamnatocin a watan Afrilu. Rahoton tace naira biliyan 446,65 ya fito ne daga asusun bai daya, naira biliyan 92.18 daga asusun harajin da ake daurawa a cinikayya na VAT, naira biliyan 10 daga asusun NNPC, biliyan 13.09 daga asusun canjin kudin kasashen waje sai kuma naira biliyan 55 daya fito daga asusun harajin kaya.

  Haka zalika rahoton ya fayyace gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 257.76, jahohi 36 sun samu biliuan 168.25 yayin da kananan hukumomi suka samu biliyan 126.58, babban birnin tarayya Abuja ta samu naira biliyan 5.49, sai kuma naira biliyan 49.82 aka raba ma jahohi masu arzikin man fetir a matsayin hakkinsu na kashi 13. 

  Bugu da kari gwamnati ta baiwa hukumar tattara haraji ta kasa FIRS, naira biliyan 6.15, hukumar yaki da fasa kauri ta kwastam naira biliyan 5.12 da kuma hukumar kula da arzikin man fetir ta DPR naira biliyan 3.87 a matsayin kudin gudanar da ayyukan karbar haraji. Read more: https://hausa.legit.ng/1239918-gwamnatin-tarayya-jahohi-da-kananan-hukumomi-sun-kasafta-naira-biliyan-617.html
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnatin tarayya, jahohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan 617 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama