Legit Hausa
Gwamnan JIhar Kano, Abdullahi Ganduje ya nada sabbin
sakatarori 36 na hukumomi, ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati da ke jihar. A cewar
sanarwar da shugaban ma'aikatan jihar, Auwal Na'iya ya bayar, "anyi sabbin
nadin ne domin tabbatar da cimma sabbin burin gwamnatin jihar na inganta aiki
da yiwa al'umma hidimma".
A ranar 2 ga watan Mayu ne Gwamna Ganduje ya sallami dukkan
sakatarorin gwamnatin jihar inda ya bukaci su mika takardun ajiye aikinsu kafin
ranar Laraba 8 ga watan Mayu.
A wasikar da gwamnan ya aike a ranar 2 ga watan Mayu, ya
bukaci su mika takardun ajiye aikinsu ga manyan direktocin hukumominsu ko
cibiyoyi.
Gwamnan ya kuma umurci dukkan direktoci da ke mataki na 16
ko 17 da manyan sakatarorin da aka sauke daga mukamansu da ke sha'awar darewa
kan kujerar su mika takardun karatunsu da aiki zuwa ga ofishin shugaban
ma'aikata zuwa kafin karfe hudu na yammacin ranar Alhamis 9 ga watan Mayun
2019Ga cikaken sunayen sabbin sakatarorin da Ganduje ya nada:
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi