Legit Hausa
Daruruwan mutanen Kano sun yi dafifi
da yammacin ranar Lahadi zuwa filin jirgin domin nuna soyayyar su da kauna ga
sarki Sanusi II bayan gwamnatin jihar Kano ta raba masarautar Kano zuwa gida
biyar.
Ana rade-radin cewar za a iya samun
hargitsi saboda wasu masu goyon bayan gwamnati sun shirya gudanar da yin
gangamin nuna wa sarki Sanusi goyon bayan su a kan matakin da gwamnatin jihar
Kano ta dauka.
Kazalika, an zargi jami'an 'yan
sanda da hana dandazon jama'ar tarbar sarki Sanusi kuma tsohon gwamnan babban
bankin kasa (CBN). Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Wakili, ya
shiada wa majiyar mu cewar bai bayar da umarnin hana wasu jama'a gudanar da
taron gangami ba, matukar sun yi hakan cikin lumana da zaman lafiya.
A ranar Laraba ne gwamna Ganduje ya
rattaba hannu a kan dokar kirkirar sabbin masarautu hudu daga masarautar Kano.
A ranar Asabar ne gwamnan ya rantsar da sabbin sarakunan yanka na masarautu
hudun da aka kirkira. Sabbin masarautun su ne; Bichi, Gaya, Karaye da Rano. Ana
saka ran sarki Sanusi zai sauka a Kano da misalin karfe 4:15 na yamma, kamar
yadda majiyar fada ta sanar.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi