• Labaran yau


  Dandalin Kannywood: BMB ya caccaki manyan masana’antar shirya fina-finan Hausa


  Legit Hausa

  Fitaccen jarumin nan dandalin shirya finafinan Hausa kuma mazunin garin Jos, Bello Mohammed Bello wanda aka fi sani da General BMB ya caccaki manyan yan Kannywood akan wariya da suka nuna wa abokan sana’arsu na Jos. 

  Jarumin na martani ne ga rashin gayyatar yan Jos da ba a yi ba a yayin bikin kaddamar da sabuwar manhajar saida finafinan Hausa akan yanar gizo mai suna Northflix. An dai gudanar da taron ne otel din Bristol da ke garin Kano, taron ya samu hallartan masu shirya fina-finai da manyan jarumai da wasu masu ruwa da tsaki a harkar fim. 

  Sai dai hakan bai yiwa BMB dadi ba domin ba a gayyaci yan Jos ba, inda ya nemi sanin ko an yakice su daga Kannywood ne. Ga yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram: “Ko dai an cire Jos ne daga Kannywood! Abin cigaba yazo na Northflix an qi gayyatar mu, anyi meeting farko na loan, an gayyace ni, ni kadai nazo na har kano na dauki nauyin kaina daga transportation har hotel, amma daga baya an yi committee babu Bello babu gayyatar Bello. 

  "Kuma tare mukayi yaqin second term din @govumarganduje da zai bada loan din. Anci moriyar ganga ne an yar da kwauren koko yaya? "Ba'ayimin adalci ba, amma Allah ya buda mana ta hanyar da tafi imganci a gare ni, hanyar Allah na da yawa. MUNAFUNCI DAI UBANGIJIN SHI YAKE CI KUMA MU NA NAN A A.P.C din bana chanja aqida don kaifi daya nake.”
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dandalin Kannywood: BMB ya caccaki manyan masana’antar shirya fina-finan Hausa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama