Legit Hausa
Kimanin jam'iyyun siyasa 75 a fadin
Najeriya a ranar Litinin sun cimma matsaya tare da bayyana matakin su kan
shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, biyo bayan gudanar
babban zaben kasa na 2019.
Jam'iyyun siyasa 75 a fadin Najeriya
sun bayyana aminci tare da amanna akan kwazon shugaban hukumar INEC dangane da
samun abun da su ka bayyana a matsayin ingatacciyar nasara yayin kammala zaben
shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a ranar 23 ga watan Fabrairu da kuma
na gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a ranar 9 ga watan
Maris.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa,
jam'iyyun sun yi itifakin cewa gudanar babban zaben kasa na bana ya yi daidai
da cikar burikan mafi akasarin al'ummar Najeriya. Shugabannin jam'iyyun sun
cimma wannan matsaya a yayin wani zama na kwanaki biyu da suka aiwatar cikin
babban birnin kasar nan na tarayya domin fayyace duk wata harkalla da ta gudana
a yayin babban zabe na bana.
Sai dai jam'iyyun sun yi babbatu na
bayyana yadda hukumomin tsaro musamman dakarun soji su ka haifar da duk wata
tagarda da kuma cikas da aka fuskanta a yayin gudanar da zaben Domin kaucewa
maimacin makamancin wannan abun ki, jam'iyyun sun yi kira ga shugaban kasa
Muhammadu Buhari a kan gaggauta sanya hannu cikin sabon kudiri na sauya salon
zaben kasar nan.
Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito
cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar Sierra Leone, Alhaji Sam Sumana, ya
halarci babban taron bisa jagorancin Farfesa Remi Aiyede da aka gudanar cikin
babban dakin taron kasa da kasa na ICC da ke garin Abuja.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi