Daga zuwa biyan kudin fansa, yan bindiga sun yi garkuwa da hadimin gwamnan Katsina


Legit Hausa

Guda daga cikin tsofaffin hadiman gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, Kwamared Bashir Usman Ruwan Godiya ya fada hannun masu garkuwa da mutane da sanyin safiyar Juma’a, 31 ga watan Mayu na shekarar 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ruwan Godiya, wanda Malami ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta jahar Katsina, ya fada hannun yan bindigan ne a yayin da yaje wajensu domin biyan kudin fansan wani abokin aikinsu da yan bindigan suka yi garkuwa dashi a ranar Alhamis.

Rahotanni suna bayyana cewa jim kadan bayan yan bindigan sun kama Ruwan godiya, sai suka tuntubi iyalansa inda suka nemi a biyasu karin kudin fansa kafin su sakoshi tare da abokin aikin nasa. Idan za’a tuna wasu gungun yan bindiga sun yi garkuwa da malamin kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman dake jahar Katsina, Dakta Bello Birchi, a gidansa dake kan titin zuwa garin Dutsanma a kauyen Tashar Bara’u cikin karamar hukumar Birchi, a daren Alhamis. 

Shugaban kungiyar Malaman kwalejin kimiyya da fasaha, Dakta Sabi’u Yau Abdullahi ne ya tabbatar da sace abokin aikin nasu, inda yace lamarin ya jefa kafatanin malaman kwalejin cikin halin dimuwa, alhini da jimami. Kimanin watanni biyu kenan yan bindiga sun tsananta kai hare hare a jahar Katsina, musamman a kananan hukumomin Kankara, Dutsanma da kuma Batsari, da kauyukan dake zagaye dasu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN