Cutuka guda 8 da aduwa take maganin su


Legit Hausa

Tun da can mutane sun dauki aduwa a matsayin sahihin magani, sai dai kuma kowacce kasa da yadda take amfani da ita da kuma yadda take sarrafa ta wurin magani, sannan kowacce kasa da irin maganin da take yi da ita. A kasar mu ta Hausa, masu magungunan gargajiya sun cinye lokaci mai tsawon gaske suna amfani da ganye da 'ya'yan aduwa wurin maganin wasu cutuka. Ga wasu daga cikin magungunan da aduwa take yi:

1. Ana amfani da garin ganyen aduwa da Ricinus Communis, a tafasa da ruwan zafi a dinga wanka dashi don magance kurajen fata, kazuwa, kunar wuta da kaikayin jiki.
2. Ana amfani da ganyen aduwa wurin magance cutar fitsarin jini.
3. Ana dafa bawon itacen aduwa a dinga shan ruwan domin maganin cutar kuturta.
4. Ana amfani da garin kwallon aduwa cokali daya a cikin kunun gero a dinga sha akan lokaci, yana maganin tsutsar ciki.
5. Ana shan ruwan ganyen aduwa idan an dafa don maganin ciwon gudawa.
6. Ana amfani da garin kwallon aduwa wurin maganin cutar asma, idan aka daka kwallon a tafasa karamin cokali guda uku a dinga sha.
7. Ana yin kunun aduwa ana sha ga mai yawan amai da tashin zuciya. Sannan ana amfani da kunun wurin maganin hawan jini, idan ana sha.
8. Mace mai shayarwa zata iya amfani da garin ganyen aduwa a cikin kunun gero, domin tsaftace jininta da cikinta, sannan za ta samu isashen nono ga jaririnta.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN