Legit Hausa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa babban sifeton
rundnunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Abubakar Adamu, da babban hafsan rundunar
sojojin Najeriya (COAS), Janaral Abayomi Gabriel Olonisakin, umarnin kafa
kwamitin da zai binciko abinda ya faru a jihar Katsina tare da mika masa rahoto
cikin gaggawa.
A sanarwar da Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaban kasa a
bangaren kafafen sadarwa na zamani, ya fitar a shafinsa na Tuwita ya ce shugaba
Buhari ya bukaci shugabannin hukumomin tsaron da su binciko yadda aka kaddamar
da hare-hare a kan wasu al'ummomi a jihar Katsina duk da kasancewar ana cikin
watan Ramadana mai alfarma.
Kazalika ya umarci su dauki matakan da zasu tabbatar da
hakan bata sak faruwa ba a nan gaba. A ranar Talata ne Legit.ng ta kawo muku
labarin cewar wasu 'yan bindiga sun kashe fiye da mutane 26 a wani hari da suka
kai a kan mazauna wasu garuruwa dake kananan hukumomin Dan Musa, Faskari da
Batsari dake jihar Katsina.
Majiyar mu ta sanar da mu cewar 'yan bindigar sun kai harin
ne ranar Talata a kan babura. A cewar majiyar, an kashe mutane 11 a garin Sabon
Layin Galadima dake karkashin karamar hukumar Faskari, yayin da aka kashe
mutane biyar a Mara Zamfarawa dake karamar hukumar Dan Musa tare da sace
dabbobi da dama. Gidan Talabijin na Channel ya rawaito cewar 'yan bindigar sun
kai wa wasu manoma hari a gonakin su a kauyen 'Yar Gamji dake karamar hukumar
Batsari, inda suka kashe mutane 18, yayin da aka rasa mutane 10.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah,
ya ce wadanda aka kashe a karamar hukumar Faskari mambobin kungiyar bijilanti
ne. A cewar sa, "wasu 'Yansakai a kauyen Sabon Layi a karamar hukumar
Faskari sun bi 'yan bindigar cikin daji tun jiya amma har yanzu basu dawo ba.
Mazauna kauyen sun samu nasarar gano gawar mutum biyu daga cikin su kuma tuni
sun binne su.
"Mun tura runduna 'yan sanda karkashin jagorancin DPO
din Faskari domin nemo ragowar kuma su ma sun yi nasarar gano karin gawar
mutane uku. Kazalika mun gano wani sansani da 'yan ta'addar suka taba amfani da
shi. Muna cigaba da gudanar da bincike," a cewar DSP Isah. A dangane da
harin Dan Musa da Batsari, DSP Isah ya ce rundunar 'yan sanda tana kokarin
samun karin bayanai. "Muna kokarin samun rahotanni har yanzu," a
cewar sa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi