Boko Haram sun bukaci Jonathan da ya Musulunta, sun aika masa da wata wasika - Clark


Legit Hausa

Wani jigon kasa, Cif Edwin Clark, ya bayyana cewa yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun aika ma Goodluck Jonathan wasika a lokacin da yake shugabancin kasa kan cewa ya musulunta. 

Clark har ila yau yace gazawan shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen yakar matsalar tsaro cikin shekaru hudu da suka gabata abu ne mai matukar damuwa. Jigon har ila yau ya kara da cewa yan ta’addan Boko Haram a kasar sun kasance da goyon bayan wasu manya daga cikin jami’an gwamnati da kuma manyan yan siyasa. 

Ya bayyana cewa wasu shuwagabannin tsaro sun halarci tattaunawan a lokaci Abba Marama, wanda kungiyar ta kama, ta kuma sako tare da wasika zuwa ga Jonathan. Jigon har ila yau yayi roko ga kungiyar ta’addan da su daina daukaka myagun ayyukanta a kasar, inda ya kara da cewa kamar yanda aka sani, Najeriya bata da wata kasa banda wanda yan ta’addan ke ciki. 

Haka zalika, Legit.ng ta rahoto a baya cewa tsohon shugaban majalisa kuma sakataren kungiyar amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Adolphus Wabara, ya bayyana cewa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dauki shawaransa na cewa kada ya tsaya takara a zaben 2015, toh da jam’iyyar bata fadi a zaben shugaban kasa ba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN