Barayin yan Najeriya za su far mun bayan 2023 - Buhari


Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu ya bukaci kotun kula da da’ar ma’aikata ta CCB, da ta adana takardar kaddamar da dukiyoyinsa da kyau, domin wadanda ke fuskantar tuhuma na cin hanci da rashawa a gwamnatinsa za su far masa bayan ya sauka daga mulki.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da shi da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo suka karbi sabon fam din kaddamar da dukiya daga Shugaban CCB, Farfesa Mohammed Isa, wanda ya jagoranci tawagar ciki harda Barista Murtala Kankia da Dr. Emmanuel Attah a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Shugaban kasar a jawabinsa yace: “Nayi farin ciki da kasancewarku a nan, Ina baku tabbacin cewa zanyi gaggawan cike wannan fam din sannan na dawo dashi gare ku saboda a karshen 2023, na san cewa akwai mutane da dama da za su so zamar dashi hujja a gaare ni. 

“Saboda haka dan Allaj ku tabbatar kun adana shi da kyau saboda akwai mutanen da suke ganin bai kamata a tuhume su ba amma kuma aka tuhume su sannan yanzu haka wasun sun a cikin matsala.
“Ina sanya ran za su ake ni sannan kuma wannan nan ne daya daga cikin makaman. Don haka ina fatan za ku ajiye shi.” Ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da yake ganin kungiyar tun bayan nadinsu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN