Legit Hausa
Alkalin kotun tarayya da ke Minna, Jastis Aminu Aliyu, a
ranar Alhamis 23 ga watan Mayu, ya bayar da umurnin kamo tsohon gwamnan Jihar
Niger, Babangida Aliyu da Umar Nasko.
Jastis Aliyu ya kume janye belin da Jastis Yellim Bogoro ya
bawa Aliyu da Nasko saboda rashin bayyana a kotu domin cigaba da sauraron
shari'ar da ake musu. Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ta ruwaito cewa
kotu ta bukaci Aliyu da Nasko su gurfana a gabanta a ranar Alhamis ne domin
sake fara sauraron shari'ar tuhumar da ake musu na damfarar Naira Biliyan 1.9
da aka mayar zuwa kotun Jastis Aliyu. Lauyansu shima bai bayyana a gaban kotu
ba. Olajide
Ayodele, lauyan Gwama Aliyu, ya aike wa kotu da wasika inda
ya roki a dage cigaba da sauraron karar. Daga karshe an dage cigaba da sauraron
karar zuwa ranar 27 ga watan Mayun 2019 kamar yadda NAN ta ruwaito
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI