Babu wanda ya isa ya hana a rantsar da ni - Tambuwal


Legit Hausa

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, a jiya Lahadi, 19 ga watan Mayu yayi zargin shirye shiryen haddasa rigingimun siyasa a jihar, kamar yanda ya jaddada cewa babu wanda ya isa ya hana a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu. 

Yayin da yake magana ta hannun babban hadiminsa, Alhaji Yusuf Dingyadi, gwamnan yayi zargin cewa wassu mutane suna yada karerayi da kuma haddasa rudani cewa kotu tana shirin tsige shi daga kujerarsa sannan ta mika mulkin ga APC. 

Ya kara da cewa an cire fostan shi da aka lika a hanyar Birnin Kebbi, hanyar tashar jirgi da Maiduguri an kuma mayar da fostan dan takaran jam’iyyar APC. Tambuwal ya karfafa cewa kotu kadai ce take da karfin hana gwamnatinsa. 

Gwamnan ya shawarci jam’iyyar adawa da ta “bar kotu ta gudanar da aikin ta, jam’iyyar PDP a Sokoto bata nemi hukunci ta kofar baya ba. Kawai a bar kotu tayi abunda ya dace, muna da tabbaci akan kotu saboda mun lashe zabe ne da ikon Allah.”
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN