Ba za mu amince da wa’azin batanci ba a watan Ramadan – APC ta gargadi malamai


Legit Hausa

Yayin da musulmai suka fara azumin watan ramadana a ranar Litinin, jam’iyyar All Progressives Congress, (APC) ta roki musulmai da su kiyayi malamai, don wannan lokacin ne ake amfani da shi wajen yada kalaman kiyayya akan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Babban sakataren sadarwa na jam’iyyar, Mallam Lanre Issa-Onilu ya bayyana gargadin a sakon watan ramadana da ya gabatar ga manema labarai. Kakakin APC din ya shawarci yan Najeriya da su kai rahoto ga hukumomi akan masu boyewa a karkashin inuwar malamta don gudanar da mugun nufi ko neman boyan bukatunsu.

Mallam Onilu wanda ya amince a wani jawabi cewa “lamarin garkuwa da mutane, ta’addanci, rikicin kabilu da na addinai da rigingimu da sauran laifuffukan da ake daukakawa a wassu yankunan kasar sun kasance abun damuwa matuka.

"Haka zalika ya yi ikirarin cewa “gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dauke da matakai mai nau’i da dama wajen ganin ta magance rigingimu sannan ya cigaba da bayyana cewa “shugaban kasar ya bada umurni ga hukumomin tsaro masu muhimmanci da su yi maganin duk wata barazana akan harkar tsaro, su kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da ke fuskantan tashin hankali.”

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN