Anyi wa wani mutumi bulala 40 kan laifi shan mangoro a watan Ramadana


Legit Hausa

Wata kotu a Jigawa a ranar Talata, 28 ga watan Mayu ta yanke wa wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila hukuncin shan bulala 40 saboda karya azuminsa da yayi a bainar Jama’a ba tare da dalili ba kuma da rana tsaka. 

Alkalin kotun, Safiyanu Ya’u ya yanke wa Isma’il wannan hukunci ne bayan hukumar Hisba ta kama shi yana shan mangoro baro-baro a bainar jama’a alhalin kowa na Azumi da gangan. Ya’u ya ce bisa ga shari’ar musulunci laifi ne babba mutumin dake da koshin lafiya ya ki yin azumin watan Ramadana ba koko ya karya haka kawai ba tare da wani dalili ba da shari’a ya tabbatar. 

Laifin ya sama na sashi 370 na dokar jihar Jigawa. Ya ce a dalilin haka za a yi wa Isma’il bulala 40 a bainar jama’a domin ya zama ma wasu darasi cewa hakan ba a yi wa addini wasa. Yace za lallasa bayan Isma;ial a Kasuwa sannan za ayi shela kowa ya fito a taru a gani. Idan aka yi masa haka zai zama darasi ga duk wadanda ke wasa da aikin ibada musamman Azumi.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN