• Labaran yau

  An samu sabani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon


  Legit Hausa

  Sabani na neman shiga tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon, bayan da ya yi wani shagube a shafinsa ita Hadiza Gabon kuma ta nuna rashin amincewarta akan maganar da yayi din Wata irin zazzafar muhawara ta barke tsakanin Naziru Ahmad Sarkin Waka da fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan Hadiza Aliyu Gabon. 

  Mawakin Naziru Ahmad, wanda Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya nada mukamin Sarkin Mawakan Kano, yayi wani shagube a shafinsa kan mutane masu yin kyauta kuma suje kafafen sada zumunta suna yadawa domin duniya ta gani. Mawakin ya ce, "Yin hakan bai kamata ba ko kadan saboda kamar izgilanci ne da cin fuska ga wanda ka bai wa sadakar idan har ka yada shi a shafin sada zumunta." 

  Sai dai kuma mawakin bai jima da wallafa sakon nashi ba, sai fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan Hadiza Aliyu Gabon ta maida masa martani inda take bayyana cewa; "Yana da kyau, kuma ya kamata idan mutane suka yi kyauta su sanya a kafafen sada zumunta domin hakan shi ne zai taimaka wurin jawo hankalin wasu suyi koyi da masu taimakawa marasa karfin." 

  Hadiza Gabon kowa yayi mata kyakkyawan sani akan taimakon gajiyayyu, marayu, da talakawa, musamman a wata irin wannan mai alfarma. Idan ba a mance ba majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton sabanin da jarumar Hadiza Gabon ta samu tsakaninta da Amina Abdullahi Amal, lamarin ya kawo cece-kuce a kafar sadarwa inda mutane da yawa suke ganin cewa abinda Hadiza gabon ta yi bai kyauta, har suke bai wa Amina Amal shawarar ta kai ta kara kotu
   

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An samu sabani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });