An rantsar da sabon gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, amma an fita dashi saboda rashin lafiya


Legit Hausa

Ana cikin bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, aka fitar da shi daga farfajiyar taron saboda rashin lafiya da yake fama da shi. Wannan abu ya faru ne a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu bayan rantsar da sabon gwamnan da mataimkainsa, Umar Kadafur. 

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa sabon gwamna, Umara Zulum, bai kai ga kammala jawabinsa na farko a matsayin gwamna ba kafin aka fitar da shi daga farfajiyar saboda gaza magana. 

Kamfanin dillanci Najeriya ta bada rahoton cewa babban alkalin jihar Borno, Kashim Zanna, ya rantsar da sabon gwamnan ne a taron da dubunnan mutan jihar Borno, shugabanni da manyan jami'an gwamnati suka halarta. Tsohon gwamnan, Kashim Shettima, ya bayyana farin cikinsa kan mika ragamar mulki ga wanda yake kyautatawa zaton mutumin arziki ne kuma kwararre wanda zai iya kawo cigaba ga jihar.
 

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN