Legit Hausa
‘Yan bindiga sun hallaka Bayin Alla
da-dama a wasu hare-hare har 3 da aka kai a cikin Garuruwan jihar Zamfara a
karshen makon jiya. Jaridar Punch ta rahoto adadin mutanen da aka kashe a
jihar. Akalla mutane 50 ne aka hallaka, bayan an ji wa wasu 31 rauni a cikin
hare-haren da aka kai cikin Zamfara kwanan nan.
Wasu ‘Yan bindiga dai sun hana
mutanen yankin Dangurgu, kunkilai, da Birnin Magaji sakat a cikin kwanakin nan.
Hari 3 aka kai a cikin wadannan Garuruwa da ke cikin kananan hukumomin Maru,
Gusau da kuma Birnin Magaji a karshen makon da ya gabata, Hakan na zuwa ne
bayan jami’an tsaro sun yi azamar kawo karshen ta’adin da ake yi a jihar.
Dakarun ‘yan sanda sun kaddamar da
wani shiri na ‘Operation Puff Adder’ da ake sa rai zai kawo karshen kashe
mutanen da ake yi a Garuruwan Zamfara da kewaye. Amma sai ga shi an kashe mutum
50 a Ranar Asabar da ta wuce. Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan ‘yan
bindiga sun shiga Kauyen Kunkilai ne a Ranar 4 ga Watan Mayun nan inda su ka
budawa wasu masu halartar bikin suna wuta.
A nan-take aka kashe mutane 30, kuma
aka raunata mutum 6. A Ranar Juma’a kuma ‘Yan bindiga su ka kashe mutum 20 a
Garin Magami da ke cikin Gusau, an kuma yi wa mutum 15 rauni a harin daga ciki
har da sojoji. Jami’an tsaro sun tabbatar da aukuwar wannan hari bayan ‘yan
bindigan sun tsere.
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi