An kama wani dattijo a Kano zai tafi Saudiyya da miyagun kwayoyi


Legit Hausa

Hukumar hana ta'ammuli da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta kama wani dattijo mai shekaru 72, Mohammed Hamza da wani Kamisu Muhammad da haramtattun kwayoyi a filin tashi da saukan jirage na kasa da kasa ta Mallam Aminu Kano (MAKIA). An damke dattijon ne yayin da ya ke kokarin shiga jirgi zuwa kasar Saudiyya.

A yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a ranar Juma'a, Kwamandan NDLEA na MAKIA, Mr Ambrose Umoru ya ce an kamane Hamza wanda dan asalin kauyen Gwaranduma ne a karamar hukumar Daura a jihar Katsina a lokacin da ake bincikar kayayakin matafiya. Sai dai dattijon ya shaidawa jami'an NDLEA cewa bai shi da masaniya a kan yadda akayi kwayoyin suka shiga jakarsa.

 "Mun gano cewa wasu ne da suka biya wa dattijon kudin jirgi zuwa kasar Saudiyya suka saka kwayoyin Tramadol a cikin jakar kayansa. Sun kawo shi Kano daga Katsina inda suka ajiye a Otel na kwanaki uku kuma a wannan lokacin ne suka saka kwayoyin jikin jakarsa ba tare da saninsa ba.

"A lokacin da jami'an mu suka gano muggan kwayoyin kuma ya fada mana inda ya fito. Ba tare da bata lokaci ba sai muka aike jami'an mu suka tsare Kamisu Mohammed. "Kamar yadda bayannan mu suka nuna, an taba kama Mohammed da laifin saka muggan kwayoyi cikin jakkunan wasu mata biyu a baya. Sai dai a wancan lokacin matan tare suke aiki da Mohammed ba kamar dattijon nan da bai san hawa ba balle sauka," inji Umoru.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN