Legit Hausa
Jami'an yadda labarai na hukumomin, Malam Yunusa Abdullahi
da Muhammad Lawal sun bayyana hakan ne a cikin sanarwar da suka fitar a Kaduna
da Abuja. Sanarwar ta ce Cibiyar Kula da Aikin Hajji na Kasa ta amince da N1,
549,297.09 a matsayin kudin kujerar aikin hajji da kowane maniyyaci zai biya
domin zuwa kasar Saudi Arabia sauke farali.
Za kuma a bawa maniyyatan allawus din tafiya na $800.00.
Abdullahi na jihar Kaduna ya ce mai sanya idanu kan hukumar Alhazai na jihar,
Imam Hussaini Ikara ya yi bayyanin cewa an cimma matsaya a kan kudin ne bayan
anyin lissafi da kudin masauki a Makkah da Madina da sauran abubuwa. "Ba a
kayyade BTA ba kamar yadda akayi a shekarun baya.
"Mutanen da suka gudanar da aikin hajji a shekaru hudu
da suka gabata za su biya kari Riyal 2000 wanda ya yi daidai na N162.000."
Sai dai Ikara ya shawarci maniyyata suyi gaggawan biyan kudin kejurun su domin
tuni an fara aikin tantance biza kuma akwai bukatar a biya cikon kudin ga
hukumar NAHCON kamar yadda aka tsara.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Tags:
LABARI