Jihar Kebbi: Abdullahi Muslim ya gudanar da shikamakin alkawari ga jama'ar da yake wakilta

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza, Alh Abdullahi Muslim, ya gudanar da karin wasu ayyukan more rayuwa a mazabar da yake wakilta wanda ya zama cika alkawari ga amanar da ya dauka ga jama'arsa.

Asibin da Abdullahi Muslim ya gina a garin Junju
Duk da yake Abdullahi Muslim yana shirin barin kujerarsa a zauren Majalisar wakilai na tarayya, amma wannan bai sa ya yi kasa a guiwa ba wajen cika alkawari da ya yi ga talakawan da ya shafe shekaraunsa na siyasa yana kyakkyawar mu'amala, hulda da kuma zamantakewa da su.

Rijiyar burtsate (Motorised borehole) a garin Nayelwa
Ayyukan da Muslim ya gudanar sun hada da gina wani Asibiti na zamani tare da samar da kayan aiki a garin Junju, da ginin rijiyar burtsatse na zamani watau Motorised borehole a unguwar zabarmawa a garin Birnin kebbi, sai kuma wata rijiyar burtsase na zamani watau motorised borehole har ila yau a garin Nayelwa, da kuma ginin dakuna uku na ajin makarantar Islamiyya da ake kan gudanarwa a unguwar Sarakuna a garin Birnin kebbi.

Ginin dakuna uku na Makarantar Islamiyya a shiyar Sarakuna B/kebbi
Hakazalika a karkashin shirinsa na samar da ingantaccen kiwon lafiyar idanu ga jama'ar mazabarsa duk da yake yana shirin barin kujerar zauren Majalisar wakilai, amma Hon. Abdullahi Muslim har ila yau, ya gudanar da shirinsa na samar da kulawa tare da bayar da magani kyauta ga masu matsalar idanu guda dubu uku (3000) a Birnin kebbi. Hakazalika Abdullahi Muslim ya bayar da kyautar buhun taki guda dubu daya da dari takwas (1800) ga matasa manoma tare da sauran jama'a guda dari shida (600) domin inganta aikin noma a mazabarsa ta Birnin kebbi, Kalgo da Bunza.
Ginin rijiyar burtsatse (Motorised borehole) a shiyar Zabarmawa B/kebbi

Majiyar isyaku.com ta ce, wadannan ayyuka basu cikin ayyukan raya mazabu da ke jaddawalin aikin dan majalisa, amma wadannan ayyuka na kwamiti ne a majalisar wakilai wanda Hon Abdullahi Muslim ya aiwatar bisa dattaku, mutunci amana tare da tsoron Allah.

Duniyar siyasar jihar Kebbi za ta tuna da Abdullahi Muslim bisa salon mutunci, hakuri ,amana da girmama talakawan Birnin kebbi, Kalgo da Bunza da ya yi , kuma yake kai a ko da yaushe. Hakazalika, jihar Kebbi za ta sake tuna Abdullahi Muslim bisa hakuri matuka da ya nuna, wanda ya kasance tubali ga nassara da ya samu a gidan siyasar jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN