Hon. Abu Najakku ya yantar da fursunoni 4 daga Kurkukun Birnin kebbi

Tsohon dan takarar kujerar Majalisar Wakilai na tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza Alh. Abu Najakku, ya kubutar da wasu fursunoni guda hudu da ke zaman gidan Kurkuku a garin Birnin kebbi bisa laifuka daban-daban bayan ya biya masu kudin tara da Kotu ta yanke hukunci a kansu.

A ranar Juma'a ne wakilan Alh.Abu Najakku wanda suka hada da Alh.Adamu Utono da Alh. Bello Sani suka jagoranci hidiman fitar da wadannan Fursunoni guda hudu a cikin watan Ramadana mai falala daga tsohon gidan Yarin Illela Yari inda aka fitar da mutum uku, sai kuma sabon gidan yari inda aka fitar da mutum daya.

Fursunonin da aka kubutar sun hada da Rilwanu Abubakar, Usman Umar, Sufiyanu Musa, da Abubakar Bashir.

Alh. Adamu Utono, ya yi wa wadanda aka kubutar nasiha jim kadan bayan fitowarsu daga Kurkuku, inda ya shawarce su a kan su gujewa aikata laifi kuma su zama mutanen kirki a cikin al'umma. Hakazalika Alh. Bello Sani, ya kara shawartarsu cewa su guji daukan doka a hannunsu ta hanyar zama mutane na gari, tare da rokon Allah ya kara kiyaye al'umma Musulmi daga kaddarori.

Wadanda aka kubutar sun yi godiya ga Allah da kuma Abu Najakku bisa wannan taimako da ya yi masu. Daya daga cikinsu Abubakar Bashir ya ce " Gaskiya na gode kwarai da Allah ya sa wannan bawan Allah ya taimake ni ya fitar da ni, ina cike da farin ciki, kuma shi ma Allah ya ya taimake shi fiye da yadda ya taimake mu domin zatin Annabi".

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN