Abinda ya kamata ka yi idan ATM yaki biyan ka kudi


Legit Hausa

Abune wanda kan dau tsawon lokaci kafin ya faru amma sai dai wani lokacin idan mutane sukayi amfani da ATM su kan samu matsalar rashin fitar kudi duk da cewa zaka samu sako daga bankinka cewa ka fitar da kudin.

Wasu lokutan matsalace ke sa ATM din ya hanaka kudi, a wani lokacin kuma idan abin ya shafi yaudarar yan damfarane hakan ke faruwa.

Duk da cewa ana mangance irin wannan matsaloli a ko da yaushe sai dai kuma akwai kosawa da mutum kan iya yi kafin a warware matsalar. A wasu lokuta bankin naka zasu san da matsalar kuma su gyara maka ba tare da ka kirasu a waya ba.

Wani lokacin kuwa abun ya kan sha ban-ban. A don haka abu mafi da cewa shine idan ka samu matsalar rashin fitar kudi daga ATM kayi gaggawar sanar da bankinka. Haka zalika, idan hart a kama zaka iya daukan bayanin ATM din da kayi amfani dashi a matsayin shaida.

Ana iya daukar hoton ATM din ma don akasarin bankuna suna sanya jerin ATM ne a wuri guda. Harwa yau akwai bukatar shi mai amfani da katin ya tabbatar cewa ATM din ya sanya kati nasa yayi daidai da irin katin.

Idan aka samu sabani hakan zai iya haifar da matsala. Tarin duk wadannan bayanai ne zai baiwa banki damar wareware bakin zaren wannan matsala.

 DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN