Abinda ake gudu ya afku: Zirga-zirga ta ragu a fadar sarkin KanoLegit Hausa

Zirga-zirga ta ragu a fadar Sarkin Kani, Muhammad Sanusi II, bayan kaddamar da sababbin masarautun yanka guda hudu da gwamna Ganduje ya yi wanda suka hada da Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya. 

Ranar Lahadin da ta gabata fadar a cike take da al'umma a lokacin da sarkin ya dawo daga aikin Umrah, inda dubunnan mutane suka fito suna yi mishi barka da zuwa a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano. 

Mutanen sun biyo shi har zuwa fadar shi daga filin jirgin, inda suke yi mishi kirarin 'Sarki Mai Martaba'. Mun samu labarin cewa a yau Talatar nan zirga-zirga ta ragu sosai a fadar, duk yawan zirga-zirgar da aka saba gani a fadar ta mutane da ababen hawa komai ya ragu.

Mutane kalilan ne suka rage a fadar sai ma'aikatan fadar. Wani Dogari wanda ya yi magana da manema labarai ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da cewar sarkin ya zabi ya kadaice kanshi tun dawowar shi daga kasa mai tsarki.


DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN