A karon farko, Kogunan Gusau ya yi magana kan ibtila'in rasa kujerarsa


Legit Hausa

Dan takarar kujera gwamnan jihar Zamfara karkashin jam'iyyar All Progressive Congress APC kuma wanda ya lashe zaben, Mukhtar Shehu, ya yi magana karo na farko bayan kwace kujerarsa da kotun koli tayi ranan Juma'a, 24 ga watan Mayu, 2019. Muktar Shehu ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara da aka gudanar a ranar 23 ga watan Mayu. 2019. 

Amma sakamako rashin gudanar da zaben fidda gwani da jam'iyyar All Progressive Congress APC tayi, babban kotun Najeriya;kotun koli ta yi fatali da dukkan kuri'un aka kadawa APC a zaben bana. A jawabinsa, Muktar Shehu yace: "Lallai mulki da girma ya tabbata ga Allah kuma shi ke baiwa duk wanda ya ga dama mulki." 

"Ya ku yan'wana maza da mata a jam'iyyar APC, ina son yin amfani da wannan dama wajen mika godiyata gareku kan goyon baya da soyayyan da kuka nuna mana a wannan lokacin zaben." "Jam'iyyarmu ta lashe zabe amma doka ta kwace. Wannan abin takaici ne ga jam'iyyarmu a jihar Zamfara, amma ibtila'i ne ga hadin kanmu." 

"Ina rokon Allah ya baiwa gwamnatin da ke shigowa ikon kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fama da shi kuma ina addu'an cewa wannan nasara da suka samu, zai kawo cigaba garemu da rana gobenmuu gaba daya."
 

DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN