12 zuwa10:30 na safe: Naji dadi da Saraki bai yi gigin hawa kujerar shugaban kasa ba - Osinbajo


Legit Hausa

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu ya yi godiya ga Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki akan rashin darewa kujerar shugaban kasa kafin bikin rantsar da su. Osinbajo ya bayyana hakan ne a wani liyafar cin abincin dare da aka shirya domin karrama Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shi kansa a fadar Shugaban kasa..

A ranar Laraba ne dai aka rantsar da Buhari da Osinbajo karo na biyu . Shugaban kasar wanda zai bar kasar zuwa Makkah, kasar Saudiyya a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu domin halartan taron OIC, ya samu wakilcin mataimakin Shugaban kasa a wajen liyafar. 

“Wani abun al’ajabi ya faru a safiyar yau, ni lauya ne kuma malamin shari’a kuma na kan gwaji da tambaya ta sigar doka. “Da misalin karfe 12 da minti daya na daren jiya, zuwa 10:30 na safiyar yau 29 ga watan Mayu lokacin da aka rantsar damu a karo na biyu babu Shugaban kasa ko mataimakin Shugaban kasa. 

“Abun mamaki babu wani akasi da aka samu, komai na nan yadda yake, idan ace wani lamari zai taso, Shugaban majalisar dattawa ne zai yi aiki a matsayin Shugaban kasa. 

“Don haka, lokacin da na iso Eagle Square da safen nan, wasu za su lura cewa Shugaban majalisar dattawa dani muna ta barkwanci. “Yace dani cikin barkwanci, gwara fa kayi a hankali kaa san nine mukaddashin Shugaban kasa yanzu, don haka, muna godiya ga Shugaban majalisar dattawa da bai yi wani abun ashha ba.”
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN