Zainab Aliyu, matar da kasar Saudiya ta tsareta bisa laifi da aka yi mata sharri

Zainab Aliyu kenan tare da ma'aikatan ofishin jakadancin Najeriya a Jeddah na kasar Saudiya jim kadan bayan hukumomi sun saketa.

An kama Zainab a kasar Saudiya bayan an ga wasu ababe da aka haramta shigowa da su kasar Saudiya a cikin jakarta.

Daga bisani an gano cewa wasu batagari masu aikata laifi ta hanyar safarar miyagun kwayoyi ne suka saka kapson Tramadol a cikin jakarta a watan Disamba na 2018.

Wannan nasarara ta kasance ne bayan shugaba Buhari ya bukaci wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ya sa baki a cikin lamarin.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post