Yar hayata tana yawo zindir a cikin gidana, ina rokon Kotu ta ja kunnenta - Maigida

Daga hagu Sibanda sanye da Kwat Theresa sanye da bakar riga da shudin buje daga dama
Wani mutum mai suna Oscar Sibanda ya maka wata budurwa da ke haya a gidansa a gaban wata Kotu saboda zargin cewa budurwar tana takura rayuwarsa ta hanyar yawo a cikin harabar gida zindir.

Wannan lamari ya faru ne a sabowar Lobengula da ke gundumar Bulawayo na kasar Zimbabwe.

Shi dai Sibanda yana zaune ne tare da yar haya Theresa Kumbota, yana rokon kotu ta ja kunnen Theresa domin ta daina tubewa zindir domin tana tayar masa da hankali.

Amma Theresa ta shaida wa Kotu cewa shi mai gidan watau Sibanda, shi ne ke satar kallonta idan ta shiga wanka. Wannan lamari dai yana gaban Kotu.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN