Yansanda sun aika wasu gaggan yan fashi lahira tsakanin Abuja zuwa Kaduna

Rundunar yansandan Najeriya ta ce jami'anta sun sami nassarar kashe wasu jiga-jigan yan fashi guda tara a gandun dajin Akilu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Kakakin hukumar yansandan Najeriya Frank Mba ya ce wannan ya faru ne bayan an yi musanyar wuta tsakanin jami'an yansanda da yan fashin kuma aka kama wasu makamai daga hannun yan fashin.

Ya kuma kara da cewa dansanda guda daya ya sami raunin bindiga bayan yan fashin sun harbeshi, kuma yana jinya a wani Asibiti.

Hakazalika ya ce yansanda na kokari wajen farautar sauran yan fashin guda biyu da suka tsere.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post