• Labaran yau

  Wata daliba ta kashe kanta, saboda saurayinta ya rabu da ita


  Legit Hausa

  A ranar Larabar nan wata dalibar jami'a dake ajin farko a jami'ar jihar Kogi, Miss Rebecca Michael, ta kashe kanta, jim kadan bayan saurayinta ya rabu da ita.

  A rahoton da muka samu, dalibar ta samu damar shiga makarantar a wannan shekarar, inda ta fara karatu a fannin Philosophy a jami'ar. Marigayiyar, wacce ta kashe kanta a cikin gidan daliban, wanda ke dauke dakuna 200 a garin Lokoja, mun samu rahoton, ta mutu tana da shekaru 20 a duniya.

  Bayan ta sha guba, an garzaya da ita asibiti mafi kusa, sai dai kuma ana zuwa ta ce ga garin ku nan. An binne gawarta jiya Laraba a makabartar Lokongoma, da ke garin Lokoja. Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar ya ce har yanzu ba a gabatar da wani rahoto akan lamarin ba.

  Jami'in ya yi alkawarin bayyanawa manema labarai, yanda lamarin ya kasance da zarar ya samu rahoto akan lamarin. Ba wannan ne karo na farko da daliban suke kashe kansu ba ta hanyar shan guba ko rataye kansu. A kwanakin baya ma wata daliba a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta kashe kanta ta hanyar shan guba, saboda iyayenta suna zargin ita maiyace.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wata daliba ta kashe kanta, saboda saurayinta ya rabu da ita Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });