Hukumar yansanda a jihar Lagos ta gurfanar da wasu mutum biyu a gaban wata Kotun Majistare bisa zargin yi ma wani ma'aikacin kampanin wutan lantarki EKEDC duka.
Wadanda aka gurfanar sun hada da Fatimot Tijjani mai shekara 40 yar kasuwa, da Azeez Awesu mai shekara 18 kuma mai sana'ar aski watau Barber.
An gurfanar da su ne a gaban wata Kotun Majistare a Ikeja karkashin jagorancin Alkali M.O. Tanimola. Bayan mai gabatar da kara ya karanta masu laifi da ake tuhumarsu , wadanda ake kara basu amsa laifin ba. Sakamakon haka Alkali ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Aprilu 2019, kuma ya bayar da belinsu a kan N100.000 kowane tare da mutum biyu da za su tsaya masu.
Ana zargin wadanda ake kara cewa sun taru suka yi ma wani ma'aikacin wutan lantarki na EKEDC duka ne bayan ya yanke wutan gidansu sakamakon rashin biyan kudin wuta da kuma tarin bashi. Amma bayan ya yanke wytar ya sauko daga cabe, sai wadanda aaka yi kara suka taru suka afk masa da duka har suka raunata shi.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi