Type Here to Get Search Results !

Main event

Shugaba Buhari ya yaba da kwazon aikin Gwamnan jihar Lagos, Ambode


Legit Hausa

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo garin Abuja bayan ziyarar aiki ta yini guda da ya kai jihar Legas a ranar Laraba, inda ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka uku da ba bu makamancin su a duk fadin Najeriya.

Yayin ziyarar sa, shugaba Buhari ya kaddamar da sabuwar tashar Motocin haya ta Oshodi, sabbin hanyoyi sufuri a tashar jiragen sama da kuma wani sabon katafaren reshen lafiya na Yara da Mata mai cin gado 170 a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas.

Bayan kaddamar da muhimman ayyuka da gwamnatin jihar Legas ta aiwatar, karkashin jagorancin , shugaban kasa Buhari ya kwarara yabo gami jinjina ga gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode, inda ya bashi lambar yabo da cewa hakika ya shaida irin kwazon aiki da ya yiwa al'ummar sa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, Buhari yayin yabawa kwazon aiki na gwamna Ambode, ya kuma bayyana farin cikin sa kwarai da aniyya dangane da yadda gwamnan ya bayar da mafificiyar gudunmuwa wajen bunkasa ci gaban Najeriya bakin daya tare da daga martabar ta a idon duniya.

Cikin na sa jawaban, gwamna Ambode ya yiwa shugaba Buhari godiya ta goyon bayan maras yankewa da ya ke ci gaba da bai wa jihar Legas tun yayin kafuwar gwamnatin sa tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Baya ga gwamna Ambode, tawagar da tayi tarayya da shugaban kasa Buhari wajen kaddamar da muhimman ayyukan ta hadar da gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun da kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

Sauran tawagar 'ya tawagar sun hadar da kusoshin gwamnatin tarayya ta mambobin majalisar zantarwa da kuma majalisar tarayya, zababben gwamnan jihar Legas mai jiran gado, Mista Babajide Sanwo Olu da kuma mataimakin sa, Mista Obafemi Hamzat.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies