Saudiya ta saki Zainab Aliyu da aka kama bayan Buhari ya sa AGF ya sa baki


Legit Hausa

Hukumomin kasar Saudiyya sun saki Zainab Aliyu, matashiyar nan 'yan Najeriya da aka kama bisa zarginta da shiga da kwaya kasar saudiyya.

A jawabin da babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ya fitar, ya ce yanzu haka Zainab na ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Saudiyya. Kazalika, ya bayyana cewa hukumomin kasar Saudiyya za su saki Ibrahim Abubakar, wani dan Najeriya da ya samu irin matsalar Zainab a kasar Saudiyya.

A ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan shari'a, Abubakar Malami, da ya tabbatar da cewar hukumomin kasar Saudiyya sun saki matashiyar nan yar Najeriya, Zainab Aliyu, da aka yi kuskuren kama wa bisa zargin laifin safarar kwaya.

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama Zainab, daliba a jami'ar Maitama Sule dake Kano, a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2018 bisa zarginta da shiga da jaka dauke da kwayar 'tramol' zuwa kasar Saudiyya.

Matashiyar ta tashi zuwa kasar Sauddiya daga filin jirgin sama na Mallam Aminu domin gudanar da aikin 'umra' tare da mahaifiyarta, Maryam, da 'yar uwarta, Hajara. Babbar mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren harkokin da suka shafi kasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ce ta sanar da umarni da shugaba Buhari ya bayar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, ta kara da cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara tattauna batun sakin Zainab tare da wasu mutane biyu dake da irin matsalar da Zainab ta samu.

DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN