Na shake matar ubangidana har ta mutu domin ya koreni daga aikin tukashi - Direba

Yansanda a jihar Oyo sun cafke wani direban mota mai suna Morenikeji Adeyemi, bayan ya shake matar ubangidansa mai suna Oyewumi Ayanwale har ta mutu ranar Juma'a.

Adeyemi ya shaida wa yansanda cewa ya kashe matar ubangidansa ne domin ya sallame shi daga aikin tukinsa ba gaira ba dalili, bayan ya shafe shekara hudu yana tukashi.

Adeyemi ya kara da cewa, ya shawo kan matar ubangidansa ne bayan ya yi ta lallashinta cewa ta bari ya tukata da motarta ya kaita wajen ibada a Chochi, daga bisani ya yi amfani da wannan dama ya shaketa har ta mutu.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post