Gwamna Yari: Za a sake shiga matsin tattalin arziki a Najeriya nan ba da jimawa ba


Legit Hausa

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a sake shiga cikin matsananci matsi na tattalin arziki a Najeriya a sabuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, gwamna Yari da ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya ce Najeriya za ta fuskanci wani sabon matsi na tattalin arziki a tsakiyar shekarar 2020.

Baya ga haka gwamna Yari yayin karin haske dangane da yadda gwamnonin Najeriya suka yiwa kawunan su karatun ta nutsu tare da fahimtar cewa ciyo bashi ba zai taba kubutar da kasar nan ba daga kalubalai na tattalin arziki.

Gwamnan ya yi furucin hakan ne a ranar Litinin yayin taron kwanaki uku na budar kai ga sabbin zababbun gwamnoni da masu dawowa karo na biyu da aka gudanar a babban birnin kasar nan na tarayya.

Ya ce ba bu shakka gwamnoni su daura damara tare da kasancewa cikin shiri na bunkasa tattalin arziki a yayin fuskantar wani sabon matsin tattalin arziki da zai auku cikin kasar nan a tsakiyar shekarar 2020.

Gwamna Yari ya kuma bayar da shawarar sa ta bunkasa da inganta hanyoyin karbar haraji a cikin jihohin Najeria tare da ribatar su ta hanyoyi mafi dace na aminci domin samun madafa ta inganta jin dadin al'umma.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN