Dododo ya yi wa Isyaku barazanar sa a kamashi idan masu sayar da waya sun yi zanga-zanga

Mai watsa labarai na jam'iyar APC na jihar Kebbi Sani Dododo ya ce"Idan suka yi zanga-zanga ku kamashi domin shi ya sa suyi" Yana gaya ma wani jami'in tsaro ne da baya sanye da kayan damara wannan jawabi.

Dododo ya yi wannan barazanar ne ga Isyaku Garba a cikin ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi bayan Isyaku ya je waken SSG domin neman manya a cikin Gwamnatin jihar Kebbi su sa baki a cikin wata matsala da ake ganin ta kunno kai dangane da wasu kudi Naira miliyan arba'in da ake zargin Gwamnatin jihar Kebbi ta ba da tallafi ga masu sayar da waya da kuma gyaran wayar salula a jihar Kebbi.

Rahotanni sun ce kudin tallafi ne da Gwamnati ta bayar ta hannun Bankin Masana'antu watau Bank of industries, amma an sami kokarfe korafe daga masu sana'ar wayar salula a cikin garin Birnin kebbi bisa tsarin yadda aka raba kudin, da dama kuma basu samu ba kawo yanzu.

Marmakain fito da tsari da zai sa manya su sa baki domin samar da fahimta bisa manufa ga wadanda suke ganin ba'a yi masu daidai ba wajen rabon kudin da kuma wadanda ke korafin cewa ba'a basu ko sisi ba, sai aka mayar da lamarin abin zargi tare da dora laifi ga Isyaku Garba saboda ya kai korafin talakawan Gwamnatin jihar Kebbi ga Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi da suke ganin ba'a yi masu daidai ba.

Sakamakon haka maganar korafe korafe ya yi kwanciyar tilas domin wadanda ya kamata su sa baki sun ki, su kuma talakawa masu korafe-korafe aka hanasu yin zanga-zanga domin Dododo ya yi wa Isyaku barazanar sa jami'ai su kamashi.

Tuni Isyaku Garba ya wanke kanshi ga talakawan da ake zargin an yi masu ba daidai ba, kuma aka hana su yin zanga-zanga. Yayin da yake jawabi ga wasu masu sayar da wayar salula a babban kasuwar Birnin kebbi ranar Alhamis, Isyaku ya ce " Bayan abin da ya faru jiya Laraba da yamma kamar yadda na sami labari, na je ofishin Sakataren Gwamnati yau domin in sami karin bayani dangane da korafe-korafen da wasu masu sayar da waya suka yi dangane da N40 miliyan da Gwamnati ta bayar, amma sai aka dora mani laifi cewa ni na zuga ku domin ku yi zanga-zanga.

" Don Allah kafin ku yi zanga-zanga kun gan ni? mun yi wata maga da ku? na ce ku yi? amma Dododo ya ce idan kun yi zanga-zanga zasu ce ni ne na sa ku saboda haka zasu sa a kama ni".

"Bana tsoron kama ni daga Gwamnatin jihar Kebbi, amma na roke ku don Allah kada ku yi wannan zanga-zanga domin kada ku ba wasu mutane damar su ci mutunci ku da ni kaina da ban ji ban gani ba kuma aka dora mani wannan laifi".

Idan dai har Gwamnatin jihar Kebbi zata taimaka wa talakkawanta da Naira Biliyan daya wanda aka raba wa kungiyoyi ta hannun Bankin masana'antu, bai kamata domin Naira miliyan arba'n da aka ba masu sayarwa da gyaran waya ya zama matsala ba. Domin kamata ya yi a saka ma Gwamnati ta hannayar yin adalci da kyakkyawar tsari wajen tafiyar da rabon wadannan kudaden tallafi wanda ba kyauta bane bashi ne da za a biya a cikin watanni 46.

Isyaku ya kara da cewa " Ni dai na tsani rashin adalci da rashin gaskiya, haka Allah ya yi ni, ban cin amanar zamantakewa kuma ban barin a ci amanar zamantakewa idan ina wajen. Amma wadanda ke korafe-korafe a kaina sai ka bincika ka gani ko akwai wani rashin adalci da suke yi wanda na bukaci a gyara. Shi mai fadin gaskiya mutum ne da Duniyar yau bata sonsa, don an tsani duk mai fadin gaskiya a cikin al'umma. Amma na bar masu kulla mani sharri ga karfin zatin Allah wanda shi ne zai yi mani magani da yardar Allah".

Idan baku manta ba, wani mutum ya yi wa Isyaku barazanar cewa ya kwashe kayansa ya bar jihar Kebbi kafin ya dawo daga Abuja a bara, yanzu kuma ga barazanar kamu daga hadimin Gwamnan jihar Kebbi a kan lamari da ya shafi neman adalci.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN