Dara ta ci gida: An kama yansanda 5 da ake zargin sun kashe wata mata

Rundunar yansandan jihar Lagos ta kama jami'anta guda biyar wadanda ake zargin sun harbi wata mata mai suna Ada Ifeanyi yar shakara 20 da bindiga a Ajegunle ranar Asabar.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Lagos DSP Bala Elkana ya ce ana zargin cewa yansandan sun kuma harbi wani mai suna Emmanuel Akomafuwa a unguwar Apapa, ya ce an garzaya Asibiti da wadanda aka harba, amma Likitoci suka tabbatar da mutuwar Ada Ifeanyi yayinda Emmanuel yake kwace a Asibiti.

Kakakin, ya kara da cewa, yansandan da ake zargin, suna aiki ne da rundunar yansanda da ke ofishin yansanda na Trinity, kuma an kamasu suna fuskantar bincike a shelkwatan yansanda da ke Ikeja a birnin Ikko, watau Lagos.

A cikin wata daya, rundunar yansandan jihar Lagos ta kori yansanda hudu tare da hukunta guda arba'in bisa samun su da aikata laifuka da suka saba ka'idar aikin yansanda.
 
DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN