• Labaran yau

  Dansanda ya bindige kanshi har lahira domin budurwarsa tana soyayya da bakanike

  Wani jami'in dansanda mai suna Constable Jackson Mwanza, ya bindige kanshi bayan ya bindige mutum biyu har lahira, ya kuma raunata mutum biyu bayan ya harbe su da bindiga kirar AK47 a Chianama na kasar Zambia, bisa zargin cewa budurwarsa mai suna Christine Mulenga tana cin amanarsa ta hanyar soyayya da awani.

  Majiyar isyaku.com ta ce Jackson ne ya dauki nauyin karatun budurwarsa Christine tun da ta gama makarantar sakandare har zuwa makaranta na gaba da sakandare. Makonni uku da suka gabata, Jackson tare da budurwarsa Christine, sun fice daga gidan da suke haya saboda Jackson ya kasa biyan kudin haya.

  Sakamakon haka sai ya laba a wajen abokansa, ita kuma Christine ta laba a wajen kawarta, inda a nan ne ta fara cin amanar saurayinta Jackson Mwanza bayan ta fara soyayya da wani bakanike, wanda ganin haka ke da wuya Jackson ya bindige bakaniken da bindiga har lahira, ya harbi kawar budurwarsa da bindiga a kafada, ya kashe mutum biyu, kuma ya raunata wasu mutum biyu kafin ya juya bindigar ya bindige kanshi har lahira.

  Wata majiya ta kara da cewa, budurwar Jackson har ila yau, bayan soyayya da take yi da wannan bakanike, hakazalika tana soyayya tare da wani saurayi a makaranta da Jackson ya ke biya mata kudi a Chianama.

  Yanzu haka yansanda sun damke Cristine suna yi mata tambayoyi dangane da hakikanin abin da ya faru da ya sa Constable Jackson Mwanza ya kashe kanshi.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dansanda ya bindige kanshi har lahira domin budurwarsa tana soyayya da bakanike Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });