• Labaran yau

  Bayyanar juna biyu bayan mutuwar aure: Wata matashiya, Bilkisu ta shigar da karar tsohon mijin ta


  Legit Hausa

  Bilkisu Aminu, wata matashiya mai shekaru 28, ta shigar da karar tsohon mijinta, Muhammad Jibril, a gaban wata kotun shari'a da ke Magajin Gari a Kaduna a kan kin amincewa da juna biyu da take dauke da shi.

  Bilkisu, mazauniyar cikin garin Kaduna, ta shaida wa kotun cewar ta zauna tare da Jibril na tsawon wata uku kafin daga bisani aurensu ya mutu.

  "Ya sake ni a ranar 6 ga watan Fabrairu, amma bayan nayi kwana biyu a gida sai na yanke shawarar zuwa asibiti domin a yi min gwaji, bayan an yi gwajin ne likita ya tabbatar min cewar ina dauke da juna biyu.

  "Amma bayan na kira Jibril na sanar da shi maganar juna biyun, sai ya ce zai ziyarce ni amma har yanzu shiru," a cewar Bilkisu. Jibril, mai shekara 32, mazaunin titin Zaria a garin Kaduna, ya shaida wa kotun cewar juna biyun ba nasa ba ne.

  Ya ce bai sadu da Bilkisu ba a tsawon watanni biyu da su ka zauna tare. "Bamu taba kwanciyar aure tare ba a 'yan watannin da muka yi tare. Saboda yawan matsalolin da ke tsakanin mu, a cikin wata na uku da auren mu ne na sake ta," a cewar Jibril.

  Alkalin kotun, Musa Sa'ad-Gona, ya bayar da umarnin a raka tsofin masoyan asibiti domin gudanar da gwajin juna biyu a kan Bilkisu kafin ya fara sauraron karar ranar Alhamis mai zuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

   DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

   Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bayyanar juna biyu bayan mutuwar aure: Wata matashiya, Bilkisu ta shigar da karar tsohon mijin ta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });