• Labaran yau

  Allah ya tona asiri:An kama daya daga cikin wadanda suka yi fashin bankin Ondo bayan kashe mutum 6


  Legit Hausa

  Rundunar sojojin Najeriya a yammacin ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, ta kama daya daga cikin yan fashin da suka kai mamaya wani banki a Idoani, wani gari a jihar Ondo, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutum shida.

  An tattaro cewa sojoji ne suka kama wanda ake zargin yayinda yake kokarin tserewa daga wajen da fashin ya afku. Ana zaton mai laifin wani mamba ne a kungiyar mutum 11 da suka kai farmaki banki sannan suka sace makudan kudade.

  Television Continental ta rahoto cewa daga cikin wadanda aka kashe harda wani sufeton dan sanda, ma’aikatan bankin biyu, kwastamomi biyu da suka je cire kudi ta ATM, da kuma wasu mutane biyu a wajen. Rahoton ya kara da cewa mutum biyar sun ji rauni sannan an kai su asibiti cin gaggawa.

  A baya Legit.ng ta rahoto cewa, wasu 'yan fashi da ake yiwa lakabi da 'Daredevil' sun kaddamar da fashi da makami a wani bankin 'yan kasuwa da ke garin Idoani a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo, Kudu maso Yammacin Nigeria. Bankin, wanda ke ya ke a rukunin gidaje na Isewa, shi ne kadai banki a garin.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Allah ya tona asiri:An kama daya daga cikin wadanda suka yi fashin bankin Ondo bayan kashe mutum 6 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });