• Labaran yau

  Ajali ya yi kira: Babban mota ta kashe yarinya bayan ta biya kudin makaranta a Banki


  Legit Hausa

  A ranar Juma’a ne dalibar mai suna Balkis Adeniyi dake Tsangayar kimiyya ta Jami’ar Ibadan ta hadu da ajalinta cikin wani hatsarin daya auku akan titin Mokola-Oyo a birnin Ibadan na jihar Oyo. Wani wanda lamarin ya faru akan idonsa ya shaidawa yan jarida hatsarin yayi sanadiyar mummunan rauni ga wasu mutum biyu yayinda mashin mai taya uku wanda akafi sani da ‘Keke Napep’ ya watsa aguje cikin babbar motar zubar da shara a unguwar Leventis dake Sango cikin babban birnin jihar.

  Bugu da kari, hatsarin dai ya auku ne misalin karfe tara da rabi yayinda dalibar ke barin banki bayan da ta riga ta biya kudin makarantarta. Hakazalika, jami’an yan sanda sun bayyana lambar keken kamar haka RU 152 UP kana kuma sun fadi sanfarin ita babbar motar wato ‘MARC LAMMERTYN’. Har wa yau, zance daga bakin wani wanda wannan hatsarin ya faru akan idonsa yace, “Ita dai wannan matar ta fito ne daga banki dake

  Ajibade inda taje biyan kudin makaranta yayin da wannan abu ya faru. “Hakika an samu ganin wayarta da kuma jakarta. A dai dai wannan lokacin ne muka samu damar bincika jakarta inda muka samu katinta na Jami’ar Ibadan daga bisani kuma muka nemi iyayenta domin sanar dasu halin da yarsu ke ciki. “Su kuwa sauran mutum biyu da suka samu raunuka a kai da kafa anyi gaggawar kai su asibiti domin basu taimakon gaggawa.”

  Yayinda yake tabbatar da aukuwar wannan lamari, jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar Oyo, mai suna Olugbenga Fadeyi, ya gaskata wannan lamari inda yake cewa tabbas wannan ya hatsarin ya auku. “Ya sake cewa, DPO na ofshin yan sandan dake Mokola ne ya labarta mana wannan batu inda nan take muka fara gudanar da bincike kai tsaye akan yanda abin ya faru.”

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ajali ya yi kira: Babban mota ta kashe yarinya bayan ta biya kudin makaranta a Banki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });